2 Corinthians 11

Bulus da Manzannin Ƙarya

1Ina fata za ku yi haƙuri da ʼyar wautata. Amma, ai, kun riga kun yi haƙuri. 2Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa tsantsa. 3Sai dai ina tsoro kada yǎ zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwaʼu da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi. 4Gama in wani ya zo wurinku yana waʼazin wani Yesu dabam da wanda muka yi waʼazinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai. 5Amma a ganina waɗancan da kuke ce da su “manyan manzanni” ba su fi ni da wani abu ba. 6Mai yiwuwa ni ba horarre ba ne a magana, amma ina da sani. Mun kuwa bayyana muku wannan a sarari, ta kowace hanya.

7Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku waʼazin bisharar Allah kyauta? 8Na yi wa waɗansu ikkilisiyoyi ƙwace ta wurin karɓar taimako daga wurinsu, domin in yi muku hidima. 9Saʼad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ʼyanʼuwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka. 10Ba shakka, kamar yadda gaskiyar Kiristi take a cikina, babu wani a yankunan Akayya da zai iya hana yin taƙaman nan tawa. 11Don me? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku! 12Zan kuma ci gaba da yin abin da nake yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su. 13Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, maʼaikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. 14Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi malaʼikan haske ne. 15Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.

Bulus Ya Yi Taƙama Game da Wahalarsa

16Ina sāke faɗa: Kada wani yǎ ɗauka ni wawa ne. Amma in kun ɗauke ni haka, to, sai ku karɓe ni kamar yadda kuke karɓan wawa, domin in ɗan in yi taƙama. 17A wannan taƙamata ba na magana yadda Ubangiji zai yi ba ne, sai dai magana ce irin ta wawa. 18Da yake mutane da yawa suna taƙama irin ta duniya, ni ma haka zan yi. 19Ku kam kuna da wayo sosai, har kuna jimre wa wawaye da murna! 20Gaskiyar ita ce, kuna haƙuri da duk wanda ya sa ku bauta ko ya cuce ku ko ya more ku ko ya nuna muku isa ko kuma ya mare ku a fuska. 21Ina jin kunya in ce mun nuna kāsawa da ba mu yi waɗannan abubuwan ba!

Abin da wani yake da ƙarfin hali yin taƙama a kai, shi ne ni ma nake ƙarfin hali yin taƙama a kai. Ina magana kamar wawa ne.
22In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Israʼilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka. 23In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan ɗauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri iri. 24Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arbaʼin ɗaya babu. 25Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni. 26Na yi tafiye tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ʼyan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun alʼummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ʼyanʼuwa na ƙarya. 27Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara. 28Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi. 29Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba?

30In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina. 31Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba. 32A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yǎ kama ni. 33Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa.

Copyright information for HauSRK